Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 1:24-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Shem ya haifi Arfakshad, Arfakshad ya haifi Shela,

25. Shela ya haifi Eber, Eber ya haifi Feleg, Feleg ya haifi Reyu,

26. Reyu ya haifi Serug, Serug ya haifi Nahor, Nahor ya haifi Tera,

27. Tera ya haifi Abram, wato Ibrahim ke nan.

28. 'Ya'yan Ibrahim, maza, su ne Ishaku da Isma'ilu.

29. Ga zuriyarsu. Nabayot shi ne ɗan farin Isma'ilu, sa'an nan sai Kedar, da Abdeyel, da Mibsam,

30. da Mishma, da Duma, da Massa, da Hadad, da Tema,

31. da Yetur, da Nafish, da Kedema. Waɗannan su ne 'ya'yan Isma'ilu, maza.

32. 'Ya'ya maza na Ketura, wato ƙwarƙwarar Ibrahim, su ne Zimran, da Yokshan, da Medan, da Madayana, da Yisbak, da Shuwa. 'Ya'yan Yokshan, maza, su ne Sheba, da Dedan.

33. 'Ya'yan Madayana, maza, su ne Efa, da Efer, da Hanok, da Abida, da Eldaya. Waɗannan duka su ne 'ya'yan Ketura, maza.

34. Ibrahim shi ne mahaifin Ishaku. 'Ya'yan Ishaku, maza, su ne Isuwa da Isra'ila.

35. 'Ya'yan Isuwa, maza, su ne Elifaz, da Reyuwel, da Yewush, da Yalam da Kora.

36. 'Ya'yan Elifaz, maza, su ne Teman, da Omar, da Zeho, da Gatam, da Kenaz, da Tima, da Amalek.

37. 'Ya'yan Reyuwel, maza kuwa, su ne Nahat, da Zera, da Shamma, da Mizza.

Karanta cikakken babi 1 Tar 1