Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 1:2-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Enosh ya haifi Kenan, Kenan ya haifi Mahalalel, Mahalalel ya haifi Yared,

3. Yared ya haifi Anuhu, Anuhu ya haifi Metusela, Metusela ya haifi Lamek.

4. Lamek ya haifi Nuhu, Nuhu ya haifi Shem, da Ham, da Yafet.

5. 'Ya'yan Yafet, maza ke nan, Gomer, da Magog, da Madai, da Yawan, da Tubal, da Meshek, da Tiras.

6. 'Ya'yan Gomer, maza, su ne Ashkenaz, da Rifat, da Togarma.

7. 'Ya'yan Yawan, maza, su ne Elisha, da Tarshish, da Kittim, da Rodanim.

8. 'Ya'yan Ham, maza, su ne Kush, da Mizrayim, da Fut, da Kan'ana.

9. 'Ya'yan Kush, maza, su ne Seba, da Hawila, da Sabta, da Ra'ama, da Sabteka. 'Ya'yan Ra'ama, maza, su ne Sheba da Dedan.

10. Kush shi ne mahaifin Lamirudu wanda shi ne ya fara ƙasaita a duniya.

11. Mizrayim shi ne mahaifin jama'ar Ludawa, da Anamawa, da Lehabawa, da Naftuhawa,

12. da Fatrusawa, da Kasluhawa tushen Filistiyawa ke nan, da Kaftorawa.

13. Kan'ana shi ne mahaifin Sidon ɗan farinsa, da Het,

14. da Yebusiyawa, da Amoriyawa, da Girgashiyawa,

Karanta cikakken babi 1 Tar 1