Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 1:16-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. da Arwadiyawa, da Zemariyawa, da Hamatiyawa.

17. 'Ya'yan Shem, maza, su ne Elam, da Asshur, da Arfakshad, da Lud, da Aram, da Uz, da Hul, da Geter, da Meshek.

18. Arfakshad shi ne mahaifin Shela, Shela kuma shi ne mahaifin Eber.

19. 'Ya'ya biyu maza ne aka haifa wa Eber. Sunan ɗayan Feleg, saboda a lokacinsa ne aka karkasa duniya, sunan ɗan'uwansa kuwa Yokatan.

20. Yokatan shi ne mahaifin Almoda, da Shelef, da Hazarmawet, da Yera,

21. da Adoniram, da Uzal, da Dikla,

22. da Ebal, da Abimayel, da Sheba,

23. da Ofir, da Hawila, da Yobab. Waɗannan duka su ne 'ya'yan Yokatan, maza.

24. Shem ya haifi Arfakshad, Arfakshad ya haifi Shela,

25. Shela ya haifi Eber, Eber ya haifi Feleg, Feleg ya haifi Reyu,

26. Reyu ya haifi Serug, Serug ya haifi Nahor, Nahor ya haifi Tera,

Karanta cikakken babi 1 Tar 1