Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 7:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sulemanu ya yi shekara goma sha uku yana gina gidansa kafin ya gama shi duka.

2. Ya kuma gina wani ɗaki da katakai daga kurmin Lebanon, tsawonsa kamu ɗari, faɗinsa kuma kamu hamsin, tsayinsa kuwa kamu talatin, a bisa jeri huɗu na ginshiƙan itacen al'ul. Aka shimfiɗa katakan itacen al'ul a bisa ginshiƙan.

3. Aka rufe shi da katakan al'ul a bisa ɗakuna arba'in da biyar da suke gefe, waɗanda suke bisa ginshiƙai. Ɗakuna goma sha biyar a kowane jeri har jeri uku.

4. Aka kuma yi tagogi masu sandunan ƙarfe, jeri uku, kowace taga tana daura da 'yar'uwarta, har jeri uku.

5. Dukan ƙofofin da madogaransu murabba'i ne, taga kuma tana daura da 'yar'uwarta har jeri uku.

6. Ya yi babban shirayi mai ginshiƙai, tsawonsa kamu hamsin, faɗinsa kamu talatin. Akwai kuma wani shirayi mai ginshiƙai a gabansa.

7. Ya kuma gina shirayi ta sarauta inda zai riƙa yin shari'a, ya rufe dukan daɓenta da itacen al'ul.

8. Ya gina gidan da zai zauna a farfajiya na ciki, wajen shirayi. ya kuma gina wa matarsa, 'yar Fir'auna, gida irin wannan.

9. Aikin gine-ginen nan, an yi shi da duwatsu masu tamani tun daga tushen har zuwa rufin. Sai da aka auna duwatsun sa'an nan aka yanka su da zarto, ciki da baya daidai da juna.

10. An kafa harsashin ginin da manyan duwatsu masu tsada, waɗansu kamu takwas waɗansu goma.

Karanta cikakken babi 1 Sar 7