Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 18:27-38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. Da rana ta yi tsaka sai Iliya ya yi musu ba'a, ya ce musu, “Ku kira da babbar murya, gama shi wani allah ne, watakila yana tunani ne, ko kuwa ya zagaya ne, ko kuma ya yi tafiya. Watakila kuma yana barci ne, sai a tashe shi.”

28. Suka yi ta kira da ƙarfi bisa ga al'adarsu, suna kuma tsattsaga jikunansu da wuƙaƙe, jini yana ta zuba.

29. Suka yi ta sambatu har azahar, lokacin ba da hadaya, amma ba muryar kowa, ba amsa, ba wanda ya kula.

30. Sa'an nan Iliya ya ce wa jama'a duka su zo kusa da shi. Jama'a duka kuwa suka zo kusa da shi. Sai ya gyara bagaden Ubangiji wanda aka lalatar.

31. Ya ɗibi duwatsu goma sha biyu bisa ga yawan kabilan 'ya'yan Yakubu, wanda Ubangiji ya ce masa, “Za a kira sunanka Isra'ila.”

32. Ya kuwa gina bagade da duwatsun da sunan Ubangiji. Ya kuma haƙa wuriya kewaye da bagaden, za ta ci kamar misalin garwar ruwa guda.

33. Ya shirya itacen wuta, ya yanyanka bijimin gunduwa gunduwa, ya shimfiɗa shi bisa itacen. Sa'an nan ya ce a cika tuluna huɗu da ruwa, a kwarara a kan hadaya ta ƙonawar da kan itacen.

34. Ya kuma sa a kwarara sau na biyu, suka kwarara sau na biyun. Ya ce kuma a kwarara sau na uku, sai suka kwarara sau na ukun.

35. Ruwa kuwa ya malale bagaden, ya cika wuriyar da aka haƙa.

36. A lokacin miƙa hadaya ta maraice, sai annabi Iliya ya matso kuwa, ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Ibrahim, da Ishaku, da Isra'ila, bari ya zama sananne a wannan rana, cewa kai ne Allah a Isra'ila, ni kuma bawanka ne, na yi waɗannan abubuwa duka bisa ga maganarka.

37. Ka amsa mini, ya Ubangiji, ka amsa mini, domin waɗannan mutane su sani, kai Ubangiji, kai ne Allah, kai ne kuma ka juyo da zuciyarsu.”

38. Ubangiji kuwa ya sa wuta ta faɗo, ta cinye hadaya ta ƙonawa, da itacen, da duwatsun, da ƙurar, ta kuma lashe ruwan da yake cikin wuriyar.

Karanta cikakken babi 1 Sar 18