Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 18:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan 'yan kwanaki, sai Ubangiji ya yi magana da Iliya a shekara ta uku, ya ce, “Tafi, ka nuna kanka ga Ahab, ni kuwa zan sa a yi ruwan sama.”

2. Sai Iliya ya tafi.A lokacin kuwa yunwa ta tsananta a Samariya.

3. Ahab kuwa ya kira Obadiya, shugaban gidansa. Obadiya kuwa mai tsoron Ubangiji ne sosai.

4. A lokacin da Yezebel ta karkashe annabawan Ubangiji, Obadiya ya kwashe annabawa ɗari ya raba su hamsin hamsin ya ɓoye su a kogo, ya ciyar da su, ya shayar da su.

5. Sai Ahab ya ce wa Obadiya, “Ka tafi ko'ina a ƙasar duk inda maɓuɓɓugan ruwa suke, da inda fadamu suke duka, watakila ma sami ciyawa mu ceci rayukan dawakai da alfadarai, don kada mu rasa waɗansu.”

6. Saboda haka suka rabu biyu don su zagaya. Ahab ya bi waje guda, shi kuma ya bi ɗaya wajen.

7. Sa'ad da Obadiya yake tafiya a hanya suka yi kaciɓis da Iliya, Obadiya kuwa ya rabe da shi, sai ya rusuna ya ce, “Shugabana Iliya, kai ne kuwa?”

8. Iliya ya amsa masa ya ce, “Ni ne. Tafi, ka faɗa wa shugabanka, sarki, cewa ga ni nan.”

9. Obadiya ya ce, “Wane laifi na yi, har da za ka ba da ni a hannun Ahab ya kashe ni?

Karanta cikakken babi 1 Sar 18