Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 16:28-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

28. Omri kuwa ya rasu, aka binne shi a Samariya. Ɗansa Ahab ya gāji sarautarsa.

29. A shekara ta talatin da takwas ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, Ahab ɗan Omri ya yi sarautar Isra'ila. Ahab ɗan Omri kuwa ya yi sarautar Isra'ila a Samariya shekara ashirin da biyu.

30. Shi kuma ya aikata mugunta a gaban Ubangiji fiye da dukan waɗanda suka riga shi.

31. Da yake abu ne mai sauƙi a gare shi ya bi hanyar zunuban Yerobowam ɗan Nebat, sai ya auro Yezebel 'yar Etba'al, Sarkin Sidon, ya kuma bauta wa gunkin nan Ba'al, ya yi masa sujada.

32. Ya gina wa Ba'al bagade a matsafar Ba'al ɗin, da ya gina a Samariya.

33. Ahab kuma ya yi gunkiyan nan Ashtoret. Ahab dai ya yi abin da ya sa Ubangiji, Allah na Isra'ila, ya yi fushi fiye da dukan sarakunan Isra'ila waɗanda suka riga shi.

34. A cikin kwanakinsa, Hiyel mutumin Betel ya gina Yariko. Ya yi hasarar ɗan farinsa, Abiram, sa'ad da ya kafa harsashin ginin, ya kuma yi hasarar autansa, Segub, sa'ad da ya sa ƙofofin, kamar yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin Joshuwa ɗan Nun.

Karanta cikakken babi 1 Sar 16