Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 15:20-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Ben-hadad kuwa ya yarda da maganar sarki Asa. Ya kuwa aiki shugabannin sojojinsa su yi yaƙi da garuruwan Isra'ila. Su kuwa suka tafi, suka ci Iyon, da Dan, da Abel-bet-ma'aka, da dukan Kinneret, da dukan ƙasar Naftali.

21. Da Ba'asha ya ji labari, sai ya daina ginin Rama, ya tafi ya zauna a Tirza.

22. Sa'an nan sarki Asa ya gayyaci dukan jama'ar Yahuza, ba wanda aka ɗauke wa. Suka tafi suka kwashe duwatsu da katakai waɗanda Ba'asha yake ginin Rama da su. Da su sarki Asa ya gina Geba ta Biliyaminu, da Mizfa.

23. Sauran dukan ayyukan Asa, da dukan ƙarfinsa, da dukan abin da ya yi, da garuruwan da ya gina, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza. Amma da ya tsufa, sai ya sami ciwo a ƙafafunsa.

24. Asa kuwa ya rasu, aka binne shi a Urushalima, Ɗansa Yehoshafat ya gāji sarautarsa.

25. Nadab ɗan Yerobowam ya ci sarautar Isra'ila a shekara ta biyu ta sarautar Asa Sarkin Yahuza. Ya yi sarautar Isra'ila shekara biyu.

26. Ya yi wa Ubangiji zunubi kamar yadda tsohonsa ya yi, ya kuma sa Isra'ila su yi zunubi.

27. Ba'asha ɗan Ahija kuwa daga gidan Issaka ya yi wa Nadab maƙarƙashiya, ya kashe shi a Gibbeton ta Filistiyawa, gama Nadab da mutanen Isra'ila sun kewaye Gibbeton da yaƙi.

28. Haka Ba'asha ya kashe Nadab a shekara ta uku ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, ya kuwa ci sarautar a maimakonsa.

Karanta cikakken babi 1 Sar 15