Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 15:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A shekara ta goma sha takwas ta sarautar sarki Yerobowam ɗan Nebat, Abaija ya sarauci mutanen Yahuza.

2. Ya yi mulki shekara uku a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Ma'aka, 'yar Absalom, wato kakarsa.

3. Shi kuma ya aikata dukan irin zunubai da tsohonsa ya yi. Bai yi aminci ga Ubangiji Allahnsa sosai, kamar yadda kakansa, Dawuda, ya yi ba.

4. Amma duk da haka, saboda Dawuda, Ubangiji Allahnsa ya ba shi fitila a Urushalima da ya sa ɗansa ya gāje shi, ya kuma kafa Urushalima,

5. domin Dawuda ya aikata abu mai kyau a gaban Ubangiji. Bai ƙetare umarnin da Ubangiji ya ba shi ba dukan kwanakin ransa, sai dai a kan Uriya Bahitte.

6. Akwai yaƙi tsakanin Abaija da Yerobowam dukan kwanakin ransa.

7. Sauran ayyukan Abaija da dukan abin da ya aikata, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.

8. Abaija ya rasu, suka binne shi a Urushalima. Ɗansa Asa ya gāji sarautarsa.

9. A cikin shekara ta ashirin ta sarautar Yerobowam Sarkin Isra'ila, Asa ya sarauci jama'ar Yahuza.

10. Ya yi shekara arba'in da ɗaya yana sarauta a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Ma'aka, 'yar Absalom, wato kakarsa.

Karanta cikakken babi 1 Sar 15