Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 14:19-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Sauran ayyukan Yerobowam, da yaƙe-yaƙensa, da yadda ya yi mulki, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.

20. Yerobowam ya yi mulki shekara ashirin da biyu sa'an nan ya rasu, aka binne shi. Ɗansa Nadab ya gāji sarautarsa.

21. Rehobowam ɗan Sulemanu ya yi mulki a Yahuza. Yana da shekara arba'in da ɗaya sa'ad da ya ci sarauta. Ya kuwa yi shekara goma sha bakwai yana sarauta a Urushalima, birnin da Ubangiji ya zaɓa daga cikin kabilan Isra'ila duka, domin ya sa sunansa ya kasance a wurin. Sunan tsohuwarsa Na'ama, ita kuwa Ba'ammoniya ce.

22. Mutanen Yahuza suka yi wa Ubangiji zunubi. Suka tsokane shi ya yi fushi saboda zunuban da suka aikata fiye da abin da kakanninsu suka yi.

23. Gama su ma sun gina wa kansu wuraren tsafi a tuddai, da ginshiƙai, da gumaka a tuddai, da cikin duhuwar itatuwa.

Karanta cikakken babi 1 Sar 14