Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 13:13-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Ya ce musu su ɗaura wa jakinsa shimfiɗa. Sai suka ɗaura wa jakin shimfiɗa, shi kuwa ya hau,

14. ya bi bayan annabin nan da ya fito daga Yahuza, ya same shi yana zaune a gindin itace oak. Ya tambaye shi, “Ko kai ne annabin da ya zo daga Yahuza?”Mutumin ya amsa, “I, ni ne,”

15. Sa'an nan ya ce masa, “Zo mu tafi gida ka ci abinci.”

16. Amma annabin ya ce, “Ba zan koma tare da kai ba, ba kuwa zan shiga gida ba, ko in ci abinci, ko in sha ruwa tare da kai a wannan wuri,

17. gama Ubangiji ya ce mini kada in ci abinci, ko in sha ruwa a can, ko in koma ta hanyar da na zo.”

18. Sa,an nan tsohon annabin ya ce masa, “Ai, ni ma annabi ne kamarka. Ubangiji ya yi mini magana ta bakin wani mala'ika, ya ce mini in komar da kai gidana don ka ci abinci, ka sha ruwa.” Amma ƙarya ce ya yi masa.

19. Saboda haka sai annabin ya koma tare da shi, ya ci abinci, ya sha ruwa a gidan tsohon annabin.

20. Sa'ad da suke zaune wurin ci, sai maganar Ubangiji ta zo ga tsohon annabin da ya komar da annabin Allah,

21. sai ya kira annabin Allah, wanda ya zo daga Yahuza, ya ce, “Ubangiji ya ce, ‘Da yake ba ka yi biyayya da maganar Ubangiji ba, ba ka kuma kiyaye umarnin da Ubangiji Allahnka ya umarce ka da shi ba,

22. amma ka komo, ka ci abinci, ka sha ruwa a wurin da ya ce maka, kada ka ci abinci, ko kuwa ka sha ruwa, saboda haka ba za a binne gawarka a kabarin kakanninka ba.’ ”

Karanta cikakken babi 1 Sar 13