Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 12:20-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Da dukan mutane suka ji, cewa Yerobowam ya komo, sai suka aika a kirawo shi ga taron jama'a. Suka naɗa shi Sarkin Isra'ila duka. Ba wanda ya bi gidan Dawuda, sai dai kabilar Yahuza.

21. Da Rehobowam ya komo Urushalima, sai ya tara dukan jama'ar gidan Yahuza, da na kabilar Biliyaminu. Aka sami mayaƙa dubu ɗari da dubu tamanin (180,000) waɗanda za su yi yaƙi da gidan Isra'ila, don su komar da su a ƙarƙashin mulkin Rehobowam, ɗan Sulemanu.

22. Amma Ubangiji Allah ya yi magana da annabi Shemaiya,

23. ya faɗa wa Rehobowam ɗan Sulemanu, Sarkin Yahuza, da dukan mutanen gidan Yahuza da na Biliyaminu, da sauran jama'a,

24. Ubangiji ya ce, “Kada ku haura zuwa yaƙi da 'yan'uwanku, mutanen Isra'ila, sai kowa ya koma gidansa, gama wannan al'amari daga wurina ne.” Su kuwa suka yi biyayya da maganar Ubangiji, suka koma gida.

25. Sa'an nan sarki Yerobowam ya gina Shekem a ƙasar tudu ta Ifraimu, ya zauna can. Daga can kuma ya tafi ya gina Feniyel.

26. Yerobowam kuwa ya ce a zuciyarsa, “Mulkin fa zai koma gidan Dawuda.

27. Idan mutanen nan sun ci gaba da zuwa Urushalima don miƙa wa Ubangiji hadayu, zuciyarsu za ta koma kan sarki Rehobowam, na Yahuza, za su kashe ni, su koma wurinsa.”

28. Sai sarki Yerobowam ya yi shawara, ya siffata 'yan maruƙa biyu da zinariya. Sa'an nan ya ce wa jama'arsa, “Zuwanku Urushalima ya isa, yanzu ga allolinku, ya Isra'ilawa, waɗanda suka fito da ku daga ƙasar Masar.”

29. Ya kafa siffar maraƙi ɗaya a Betel, ɗayan kuma a Dan.

Karanta cikakken babi 1 Sar 12