Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 31:9-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Suka yanke kansa, suka tuɓe makamansa. Suka aika manzannin a ƙasar Filistiyawa da suke kusa don su kai wannan albishir zuwa ga haikalin gumakansu, da mutanensu.

10. Suka ajiye makaman Saul cikin haikalin gumakan nan Ashtarot. Suka ɗaure gawarsa a kan garun Bet-sheyan.

11. Da mazaunan Yabesh-gileyad suka ji abin da Filistiyawa suka yi wa Saul,

12. sai dukan jarumawa suka tashi, suka yi tafiya dukan dare. Suka ɗauko gawar Saul da gawawwakin 'ya'yansa daga kan garun Bet-sheyan. Da suka zo Yabesh sai suka ƙone su a can.

13. Suka binne ƙasusuwansu a gindin itacen tsamiya a Yabesh, sa'an nan suka yi azumi kwana bakwai.

Karanta cikakken babi 1 Sam 31