Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 27:9-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Dawuda yakan fāɗa wa ƙasar, ya hallaka ta, ba zai bar mace ko namiji da rai ba. Ya kuma kwashe tumaki, da shanu, da jakai, da raƙuma, da tufafi, ya komo zuwa wurin Akish.

10. Idan Akish ya tambayi Dawuda, “A ina ka kai hari yau?” Sai ya ce, “Na kai hari a Negeb ta Yahuza, ko Negeb ta Yerameyel, ko Negeb ta Ƙan'aniyawa.”

11. Dawuda bai bar mace ko namiji da rai ba, wato da zai kawo labari, a Gat, domin yana gudun kada su faɗi abin da yake yi, su ce, “Ga abin da Dawuda ya yi.” Abin da Dawuda ya yi ta yi ke nan a lokacin da yake zaune a ƙasar Filistiyawa.

Karanta cikakken babi 1 Sam 27