Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 27:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Dawuda ya yi tunani a ransa, ya ce, “Wata rana Saul zai kashi ni, don haka ba abin da ya fi mini, sai in tsere zuwa ƙasar Filistiyawa. Sa'an nan Saul zai fid da zuciya ga nemana a ƙasar Isra'ila. Zan kuwa tsira daga hannunsa.”

2. Dawuda ya tashi tare da mutum ɗari shida da suke tare da shi zuwa wurin Akish, ɗan Mawok, Sarkin Gat.

3. Dawuda da mutanensa da iyalansu suka zauna tare da Akish a Gat. Dawuda yana tare da matansa biyu, Ahinowam Bayezreyeliya, da Abigail Bakarmeliya, wadda Nabal mijinta ya mutu.

4. Da Saul ya ga Dawuda ya tsere zuwa Gat, bai ƙara fita nemansa ba.

5. Dawuda ya ce wa Akish, “Idan na sami tagomashi a wurinka, ka ba ni wurin zama daga cikin garuruwanka na karkara domin in zauna a can. Gama me zai sa baranka ya zauna tare da kai cikin birni sarauta?”

Karanta cikakken babi 1 Sam 27