Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 24:10-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. To, yau da idanunka ka ga yadda Ubangiji ya bashe ka a hannuna a kogon, har waɗansu suka ce mini in kashe ka, amma na ji tausayinka. Na ce, ‘Ba zan miƙa hannuna in kashe ubangijina ba, gama shi keɓaɓɓe na Ubangiji ne.’

11. Baba, duba, ga shafin rigarka a hannuna. Tun da yake na yanki shafin rigarka ban kuwa kashe ka ba, sai ka sani ba ni da niyyar yi maka mugunta. Ban yi maka laifi ba, ko da yake kana farautar raina.

12. Ubangiji dai zai shara'anta tsakanina da kai, ya sāke mini, amma hannuna ba zai taɓa ka ba.

13. Mutanen dā suna da karin magana cewa, ‘Daga cikin masu mugunta mugunta take fitowa.’ Hannuna dai ba zai taɓa ka ba.

14. Shin, sawun wa Sarkin Isra'ila yake bi? Wane ne kuma kake runtuma? Kana bin sawun mataccen kare, da sawun tunkuyau?

15. Ubangiji ne zai zama alƙali, ya hukunta tsakanina da kai. Zai tsaya mini, ya cece ni daga hannunka.”

16. Da Dawuda ya gama faɗa wa Saul wannan magana, sai Saul ya ce, “Ɗana, Dawuda, muryarka ke nan?” Ya yi kuka da ƙarfi.

17. Sa'an nan ya ce wa Dawuda, “Ka fi ni adalci, gama ka yi mini alheri, ni kuwa na yi maka mugunta.

18. Yau ka nuna a sarari yadda ka yi mini alheri. Ubangiji ya bashe ni a hannunka, amma ba ka kashe ni ba.

19. Idan mutum ya sami maƙiyinsa, zai bar shi ya tafi lafiya? Ubangiji ya sāka maka saboda alherin da ka yi mini yau.

20. Yanzu kuwa na sani za ka zama sarki, sarautar Isra'ila za ta kahu a hannunka.

21. Sai ka rantse mini da Ubangiji, cewa ba za ka hallaka zuriyata a bayana ba, ba kuwa za ka shafe sunana daga cikin gidan ubana ba.”

22. Dawuda kuwa ya yi wa Saul alkawari.Sa'an nan Saul ya koma gida, amma Dawuda da mutanensa suka koma wurin ɓuya.

Karanta cikakken babi 1 Sam 24