Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 22:13-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Saul ya ce masa, “Me ya sa ka yi mini maƙarƙashiya, kai da ɗan Yesse, da yake ka ba shi abinci, da takobi, ka kuma roƙar masa Allah, ga shi yanzu, ya tayar mini, yana fakona, kamar yadda yake yi a yau?”

14. Ahimelek kuwa ya ce wa sarki, “Daga cikin barorinka duka wa yake da aminci kamar Dawuda? Wane ne surukin sarki? Wane ne shugaban jarumawanka, wanda ake girmamawa a gidanka?

15. Yau ne na fara roƙar masa Allah? A'a, kada dai sarki ya zargi baransa ko gidan mahaifina duka, gama baranka bai san kome a kan wannan ba.”

16. Sai sarki ya ce, “Hakika, mutuwa za ku yi, Ahimelek, kai da dukan gidan mahaifinka.”

17. Ya ce wa matsara da suke tsaye kewaye da shi, “Ku fāɗa wa firistocin Ubangiji, ku kashe su gama suna goyon bayan Dawuda, ga shi, sun sani ya gudu, amma ba su faɗa mini ba.” Amma barorin sarki ba su yarda su fāɗa wa firistocin Ubangiji ba.

18. Sa'an nan sarki ya ce wa Doyeg, “Kai ka fāɗa wa firistocin.” Sai Doyeg, mutumin Edom, ya faɗa wa firistocin, ya kashe mutum tamanin da biyar waɗanda suke saye da falmaran na lilin a wannan rana.

19. Ya kuma hallaka Nob birnin firistoci, ya kashe dukan mata, da maza, da yara, da jarirai, da shanu, da jakai, da tumaki.

20. Amma Abiyata ɗaya daga cikin 'ya'yan Ahimelek, ɗan Ahitub, ya tsere, ya gudu zuwa wurin Dawuda.

21. Sai ya faɗa wa Dawuda Saul ya kashe firistocin Ubangiji.

22. Dawuda kuwa ya ce wa Abiyata, “A ran nan Doyeg, mutumin Edom, yana wurin, na sani lalle zai faɗa wa Saul. Ni na zama sanadin mutuwar dukan mutanen gidan mahaifinka.

Karanta cikakken babi 1 Sam 22