Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 16:12-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Yesse kuwa ya aika aka taho da shi. Ga shi kuwa kyakkyawa ne, idanunsa suna sheƙi. Sai Ubangiji ya ce wa Sama'ila, “Tashi ka zuba masa man keɓewa, shi ne sarkin.”

13. Sama'ila ya ɗauki man zaitun, ya zuba masa a gaban 'yan'uwansa. Ruhun Ubangiji ya sauko da iko a kan Dawuda tun daga wannan rana zuwa gaba. Sama'ila kuwa ya tashi, ya koma Rama.

14. Yanzu kuwa Ruhun Ubangiji ya rabu da Saul, sai Ubangiji ya sa mugun ruhu ya azabtar da shi.

15. Barorin Saul kuwa suka ce masa, “To, ga shi yanzu, Ubangiji ya sa mugun ruhu na azabtar da kai.

16. Saboda haka muna so ka ba mu izini mu tafi, mu nemo mutum gwanin kiɗan garaya, domin sa'ad da mugun ruhun nan da Allah ya sa maka, ya hau kanka, sai ya kaɗa maka garayar don ya sauka.”

17. Saul kuwa ya ce wa barorinsa. “To, sai ku samo mini mutum gwanin kiɗa, ku kawo mini shi.”

18. Sai wani daga cikin samarin ya amsa, ya ce, “Na san wani ɗan Yesse mutumin Baitalami. Shi gwanin kiɗan garaya ne, jarumi ne kuma, mayaƙi, mai lafazi, kyakkyawa, Ubangiji kuwa yana tare da shi.”

19. Sai Saul ya aiki manzanni zuwa wurin Yesse, ya ce, “Ka aiko mini da ɗanka, Dawuda, mai kiwon tumakinka.”

20. Yesse kuwa ya yi wa jaki labtu da abinci, da salkar ruwan inabi, da ɗan akuya, ya aiki Dawuda ɗansa, ya kai wa Saul.

21. Sa'an nan Dawuda ya zo wurin Saul, ya kama aiki. Saul kuwa ya ƙaunaci Dawuda ƙwarai, har Dawuda ya zama mai ɗaukar masa makamai.

22. Sa'an nan Saul ya aika wa Yesse cewa, “Ina so Dawuda. Ka bar shi ya zauna nan ya yi mini aiki.”

23. Tun daga ran nan zuwa gaba, a duk lokacin da mugun ruhun nan da Allah ya sa masa ya hau kansa, sai Dawuda ya ɗauki garaya, ya kaɗa masa. Sa'an nan mugun ruhun ya sauka, sai Saul ya wartsake.

Karanta cikakken babi 1 Sam 16