Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 12:1-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sama'ila ya ce wa jama'ar Isra'ila, “Ga shi, na kasa kunne gare ku, na kuwa yi muku abin da kuka ce mini, na naɗa muku sarki.

2. Yanzu ga sarki a gabanku, 'ya'yana maza kuma suna tare da ku. Ni na tsufa, na yi furfura, amma na yi ta kai da kawowa a cikinku tun ina yaro har zuwa yau.

3. To, ga ni nan, ku shaida a kaina a gaban Ubangiji da gaban wanda Ubangiji ya naɗa sarki. Takarkari ko jakin wa na ƙwace? Wa kuma na zalunta, ko na wulakanta? A wurin wa na karɓi hanci don in danne gaskiya? Sai ku shaida, ni kuwa zan mayar masa.”

4. Jama'a suka amsa, suka ce, “Ba ka zalunci kowa ba, ba ka wulakanta kowa ba, ba ka kuma yi wa kowa ƙwace ba.”

5. Sa'an nan ya ce musu, “Ubangiji shi ne shaida, wanda kuma ya naɗa, shi ma shaida ne a yau, cewa ba ku iske ni da laifin kome ba.”Jama'ar suka ce, “Ubangiji ne shaida.”

6. Sama'ila kuma ya ce wa jama'a, “Ubangiji ne ya sa Musa da Haruna su fito da kakanninku daga ƙasar Masar.

7. Yanzu fa ku tsaya shiru don in yi muku magana a kan ayyuka masu adalci na Ubangiji waɗanda ya aikata dominku da kakanninku.

8. Sa'ad da Yakubu da 'ya'yansa suka tafi Masar, Masarawa suka wulakanta su, sai suka kai kuka ga Ubangiji. Ubangiji kuwa ya aiki Musa da Haruna waɗanda suka fito da kakanninku daga ƙasar Masar, suka kawo su su zauna a wannan wuri.

9. Amma suka bar bin Ubangiji Allahnsu. Ubangiji kuwa ya bashe su a hannun Sisera, shugaban rundunar Yabin, Sarkin Hazor, da a hannun Filistiyawa, da kuma a hannun Sarkin Mowab, suka yāƙe su.

10. Sai suka yi wa Ubangiji kuka, suka ce, ‘Mun yi laifi domin mun bar bin Ubangiji, muka bauta wa gumakan nan Ba'al da Ashtarot, amma yanzu muna roƙonka ka cece mu daga hannun abokan gābanmu, mu kuwa za mu bauta maka.

11. Ubangiji kuwa ya aika musu da Yerubba'al, wato Gidiyon, da Barak, da Yefta, da Samson, suka cece ku daga hannun abokan gābanku ta kowace fuska. Sa'an nan kuka yi zamanku lafiya.

12. Amma da kuka ga Nahash Sarkin Ammonawa ya zo don ya yi yaƙi da ku, sai kuka ce mini, ‘Mu dai a yi mana sarki da zai sarauce mu,’ alhali kuwa Ubangiji Allahnku ne Sarkinku.

13. To, ga sarkin da kuka zaɓa nan, kuka roƙa. Ga shi, Ubangiji ya naɗa muku shi.

14. Idan za ku yi tsoron Ubangiji, ku bauta masa, ku yi biyayya da maganarsa, ba za ku karya umarnin Ubangiji ba, idan kuma ku da sarkin da yake sarautarku za ku bi Ubangiji Allahnku, kome zai zamar muku daidai.

Karanta cikakken babi 1 Sam 12