Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yak 5:4-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Ga shi kuwa, zaluncin da kuka yi na hakkin masu girbi a gonakinku yana ta ƙara, kukan masu girbin kuwa ya kai ga kunnen Ubangijin Runduna.

5. Kun yi zaman duniya da annashuwa da almubazzaranci, ashe, kiwata kanku kuka yi saboda ranar yanka!

6. Kun hukunta mai adalci, kun kuma kashe shi, bai kuwa yi muku tsayayya ba.

7. Domin haka, sai ku yi haƙuri, 'yan'uwana, har ya zuwa ranar komowar Ubangiji. Ga shi, manomi yana sa rai ga samun amfanin gona mai albarka, yana kuwa haƙuri da samunsa, har a yi ruwan shuka da na kaka.

8. Ku ma sai ku yi haƙuri, ku tsai da zukatanku, domin ranar komowar Ubangiji ta yi kusa.

9. 'Yan'uwa, kada ku yi wa juna gunaguni, don kada a hukunta ku. Ga mai shari'a a bakin ƙofa!

Karanta cikakken babi Yak 5