Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yak 5:15-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Addu'ar bangaskiya kuwa, za ta warkar da marar lafiya Ubangiji kuma zai tashe shi, in ma ya yi zunubi, za a gafarta masa.

16. Saboda haka, sai ku riƙa bayyana wa juna laifofinku, kuna yi wa juna addu'a, don a warkar da ku. Addu'ar mai adalci tana da ƙarfin aiki ƙwarai da gaske.

17. Iliya ɗan adam ne kamarmu, amma da ya nace da addu'a kada a yi ruwa, sai da aka shekara uku da wata shida ba a yi ruwa a ƙasar ba.

18. Da ya sāke yin addu'a kuwa, sai sama ta sako ruwa, ƙasa kuma ta ba da amfaninta.

19. Ya ku 'yan'uwana, in waninku ya bauɗe wa gaskiya, wani kuma ya komo da shi,

Karanta cikakken babi Yak 5