Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yak 4:4-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Maciya amana! Ashe, ba ku sani abuta da duniya gāba ce da Allah ba? Saboda haka, duk mai son abuta da duniya, yā mai da kansa mai gāba da Allah ke nan.

5. Ko kuna tsammani a banza ne Nassi ya ce, “Wannan ruhu da Allah ya sa a cikinmu yana tsaronmu ƙwarai”?

6. Allah shi yake yin mayalwacin alheri. Domin haka Nassi ya ce, “Allah yana gāba da masu girmankai, amma yana yi wa masu tawali'u alheri.”

7. Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah, ku yi tsayayya da Iblis, lalle kuwa zai guje muku.

8. Ku kusaci Allah, shi ma zai kusace ku. Ku tsarkake al'amuranku, ya ku masu zunubi. Ku kuma tsarkake zukattanku, ya ku masu zuciya biyu.

9. Ku yi nadama, ku yi baƙin ciki, ku yi ta kuka. Dariyarku tă zama baƙin ciki, murnarku tă koma ɓacin zuciya.

10. Ku ƙasƙantar da kanku ga Ubangiji, shi kuwa zai ɗaukaka ku.

11. Ya ku 'yan'uwana, kada ku kushe wa juna. Kowa ya kushe wa ɗan'uwansa, ko ya ɗora masa laifi, ya kushe wa shari'a ke nan, ya kuma ɗora mata laifi. In kuwa ka ɗora wa shari'a laifi, kai ba mai binta ba ne, mai ɗora mata laifi ne.

12. Mai ba da Shari'a ɗaya ne, shi ne kuma mai yinta, shi ne kuwa mai ikon ceto da hallakarwa. To, kai wane ne har da za ka ɗora wa ɗan'uwanka laifi?

13. To, ina masu cewa, “Yau ko gobe za mu je gari kaza, mu shekara a can, mu yi ta ciniki, mu ci riba”?

14. Alhali kuwa ba ku san abin da gobe za ta kawo ba. Wane iri ne ranku? Ai, kamar hazo yake, jim kaɗan sai ya ɓace.

15. Sai dai ya kamata ku ce, “In Ubangiji ya nufa, ya kai rai, ma yi kaza da kaza.”

16. Amma ga shi, kuna fariya ta alfarmar banza da kuke yi. Duk irin wannan fariya kuwa muguwar aba ce.

17. Saboda haka, duk wanda ya san abin da ya kamata, ya kuwa kasa yi, ya yi zunubi ke nan.

Karanta cikakken babi Yak 4