Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yak 4:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Me yake haddasa gāba da husuma a tsakaninku? Ashe, ba sha'awace-sha'awacenku ne suke yaƙi da juna a zukatanku ba?

2. Kukan yi marmarin abu ku rasa, sai ku yi kisankai. Kukan yi kwaɗayi, ku kasa samu, sai ku yi husuma da faɗa. Kukan rasa don ba kwa addu'a ne.

3. Kukan yi addu'a ku rasa, don kun yi ta da mugun nufi ne, don ku ɓatar a kan nishaɗinku.

4. Maciya amana! Ashe, ba ku sani abuta da duniya gāba ce da Allah ba? Saboda haka, duk mai son abuta da duniya, yā mai da kansa mai gāba da Allah ke nan.

5. Ko kuna tsammani a banza ne Nassi ya ce, “Wannan ruhu da Allah ya sa a cikinmu yana tsaronmu ƙwarai”?

6. Allah shi yake yin mayalwacin alheri. Domin haka Nassi ya ce, “Allah yana gāba da masu girmankai, amma yana yi wa masu tawali'u alheri.”

7. Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah, ku yi tsayayya da Iblis, lalle kuwa zai guje muku.

8. Ku kusaci Allah, shi ma zai kusace ku. Ku tsarkake al'amuranku, ya ku masu zunubi. Ku kuma tsarkake zukattanku, ya ku masu zuciya biyu.

9. Ku yi nadama, ku yi baƙin ciki, ku yi ta kuka. Dariyarku tă zama baƙin ciki, murnarku tă koma ɓacin zuciya.

10. Ku ƙasƙantar da kanku ga Ubangiji, shi kuwa zai ɗaukaka ku.

11. Ya ku 'yan'uwana, kada ku kushe wa juna. Kowa ya kushe wa ɗan'uwansa, ko ya ɗora masa laifi, ya kushe wa shari'a ke nan, ya kuma ɗora mata laifi. In kuwa ka ɗora wa shari'a laifi, kai ba mai binta ba ne, mai ɗora mata laifi ne.

Karanta cikakken babi Yak 4