Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yak 2:23-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Aka kuma cika Nassin nan da ya ce, “Ibrahim ya gaskata Allah, bangaskiyar nan tasa kuma aka lasafta ta adalci ce a gare shi,” aka kuma kira shi aminin Allah.

24. Kun ga, ashe, Allah yana kuɓutar da mutum saboda aikatawarsa ne, ba saboda bangaskiya ita kaɗai ba.

25. Ashe, ba haka kuma Rahab karuwar nan ta sami kuɓuta saboda aikatawarta ba? Wato, sa'ad da ta sauki jakadun nan, ta fitar da su ta wata hanya dabam?

26. To, kamar yadda jiki ba numfashi matacce ne, haka ma bangaskiya ba aikatawa matacciya ce.

Karanta cikakken babi Yak 2