Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yak 2:17-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Haka ma, bangaskiya ita kaɗai, ba tare da aikin da ya nuna ta ba, banza ce.

18. To, amma wani zai ce, “Ai, kai kana da bangaskiya, ni kuwa sai aikatawa.” To, nuna mini bangaskiya, taka ba tare da aikatawa ba, ni kuma in nuna maka aikatawata, tabbatar bangaskiyata.

19. Ka gaskata Allah ɗaya ne? To, madalla. Ai, ko aljannu ma sun gaskata, amma suna rawar jiki don tsoro.

20. Kai marar azanci! Wato sai an nuna maka, bangaskiya ba tare da aikatawa ba, wofiya ce?

21. Sa'ad da kakanmu Ibrahim ya miƙa ɗansa Ishaku a bagadin hadaya, ashe, ba ta wurin aikatawa ne ya barata ba?

22. Ka gani, ashe, bangaskiyarsa da aikatawarsa duka yi aiki tare, har ta wurin aikatawar nan bangaskiyarsa ta kammala.

23. Aka kuma cika Nassin nan da ya ce, “Ibrahim ya gaskata Allah, bangaskiyar nan tasa kuma aka lasafta ta adalci ce a gare shi,” aka kuma kira shi aminin Allah.

24. Kun ga, ashe, Allah yana kuɓutar da mutum saboda aikatawarsa ne, ba saboda bangaskiya ita kaɗai ba.

25. Ashe, ba haka kuma Rahab karuwar nan ta sami kuɓuta saboda aikatawarta ba? Wato, sa'ad da ta sauki jakadun nan, ta fitar da su ta wata hanya dabam?

26. To, kamar yadda jiki ba numfashi matacce ne, haka ma bangaskiya ba aikatawa matacciya ce.

Karanta cikakken babi Yak 2