Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yak 2:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya ku 'yan'uwana, kada ku nuna bambanci muddin kuna riƙe da bangaskiyarku ga Ubangijinmu Yesu Almasihu, Ubangiji Maɗaukaki.

2. Misali, in mutum mai zobban zinariya da tufafi masu ƙawa ya halarci taronku, wani matalauci kuma ya shigo a saye da tsummoki,

3. sa'an nan kuka kula da mai tufafi masu ƙawar nan, har kuka ce masa, “Ga mazauni mai kyau a nan,” matalaucin nan kuwa kuka ce masa, “Tsaya daga can,” ko kuwa, “Zauna a nan ƙasa a gabana,”

4. ashe, ba ku nuna bambanci a tsakaninku ba ke nan, kuna zartar da hukunci da mugayen tunani?

5. Ku saurara, ya 'yan'uwana ƙaunatattu. Ashe, Allah bai zaɓi matalautan duniyar nan su wadata da bangaskiya, har su sami gado a cikin mulkin nan da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba?

6. Amma, kun wulakanta matalauta! Ashe, ba masu arzikin ne suke matsa muku ba? Ba su ne kuwa suke janku zuwa gaban shari'a ba?

7. Ba kuma su ne kuke saɓon sunan nan mai girma da ake kiranku da shi ba?

8. Idan lalle kun cika muhimmin umarni yadda Nassi ya ce, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,” to, madalla.

9. Amma in kun nuna bambanci, kun yi zunubi ke nan, Shari'a kuma ta same ku da laifin keta umarni.

10. Duk wanda yake kiyaye dukkan Shari'a, amma ya saɓa a kan abu guda, ya saɓi Shari'a gaba ɗaya ke nan.

11. Domin shi wannan da ya ce, “Kada ka yi zina,” shi ne kuma ya ce, “Kada ka yi kisankai.” To, in ba ka yi zina ba amma ka yi kisankai, ai, ka zama mai keta Shari'a ke nan.

12. Saboda haka, maganarku da aikinku su kasance irin na mutanen da za a yi wa shari'a bisa ga ka'idar 'yanci.

Karanta cikakken babi Yak 2