Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yak 1:5-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. In waninku ya rasa hikima, sai ya roƙi Allah, mai ba kowa hannu sake, ba tare da gori ba, sai kuwa a ba shi.

6. Amma fa sai ya roƙa da bangaskiya, ba tare da shakka ba. Don mai shakka kamar raƙuman ruwan teku yake, waɗanda iska take korawa tana tuttunkuɗawa.

7-8. Kada irin mutumin nan mai zuciya biyu, wanda bai tsai da zuciyarsa a gu ɗaya a dukan al'amuransa ba, ya sa rai da wani abu a gun Ubangiji.

9. Ƙasƙantaccen ɗan'uwa yă yi taƙama da ɗaukakarsa.

10. Mai arziki kuma yă yi alfarma da ƙasƙancinsa, gama zai shuɗe kamar hudar ciyawa.

11. In rana ta tāke da ƙunarta, sai ciyawa ta bushe, hudarta ta kaɗe, kyanta kuma ya gushe. Haka ma mai arziki zai gushe yana a cikin tsakiyar harkarsa.

12. Albarka tā tabbata ga mai jimirin gwaji, domin in ya jure gwajin, sai ya sami kambin rai, wanda Ubangiji ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari.

13. Duk wanda ake jarabta, kada ya ce Allah ne yake jarabtarsa, gama ba shi yiwuwa a jarabci Allah da mugunta, shi kansa kuwa ba ya jarabtar kowa.

14. Amma kowane mutum yakan jarabtu in mugun burinsa ya ruɗe shi, ya kuma yaudare shi.

15. Mugun buri kuma in ya yi ciki, yakan haifi zunubi. Zunubi kuma in ya balaga, yakan jawo mutuwa.

16. Kada fa a yaudare ku, ya 'yan'uwana ƙaunatattu.

Karanta cikakken babi Yak 1