Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yak 1:20-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. don fushin mutum ba ya aikata adalci.

21. Saboda haka, sai ku yar da kowane irin aikin ƙazanta da ƙeta iri iri, maganar nan da aka dasa a zuciyarku, ku yi na'am da ita a cikin halin tawali'u, domin ita ce mai ikon ceton rayukanku.

22. Amma ku zama masu aikata maganar, ba masu ji kawai, kuna yaudarar kanku ba.

23. Don duk wanda yake mai jin maganar ne kawai, ba mai aikatawa ba, kamar mutum yake mai duba fuskarsa a madubi,

24. don yakan dubi fuskarsa ne kawai ya tafi, nan da nan kuwa sai ya mance kamanninsa.

25. Amma duk mai duba cikakkiyar ka'idar nan ta 'yanci, ya kuma nace a kanta, ya zama ba mai ji ne kawai ya mance ba, sai dai mai aikatawa ne ya zartar, to wannan shi za a yi wa albarka a cikin abin da yake aikatawa.

26. In wani yana zaton shi mai addini ne, amma bai kame bakinsa ba, sai dai ya yaudari kansa, to, addinin mutumin nan na banza ne.

27. Addini sahihi kuma marar aibu a gaban Allah Ubanmu, shi ne a kula da gwauraye mata, da marayu a cikin ƙuntatarsu, a kuma a keɓe kai marar aibi daga duniya.

Karanta cikakken babi Yak 1