Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yahu 1:3-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Ya ku ƙaunatattuna, da yake dā ma ina ɗokin rubuto muku zancen ceton nan namu, mu duka, sai na ga wajibi ne in rubuto muku in gargaɗe ku, ku dage ƙwarai a kan bangaskiyar nan da aka danƙa wa tsarkaka sau ɗaya tak, ba ƙari.

4. Gama waɗansu mutane sun saɗaɗo a cikinku, waɗanda tun zamanin dā aka ƙaddara ga hukuncin nan, marasa bin Allah ne, masu mai da alherin Allah dalilin aikata fajirci, suna kuma ƙin makaɗaicin Ubangijinmu Yesu Almasihu.

5. Sai dai ina so in tuna muku, ko da yake kun riga kun san kome sosai, cewa Ubangiji ya ceci jama'a daga ƙasar Masar, duk da haka daga baya ya hallaka waɗanda ba su ba da gaskiya ba.

6. Har ma mala'ikun da ba su kiyaye girmansu ba, amma suka bar ainihin mazauninsu, ya tsare su cikin sarƙa madawwamiya a baƙin duhu, har ya zuwa shari'ar babbar ranar nan.

7. Haka kuma Saduma da Gwamrata, da birane kewayensu, waɗanda su ma suka dulmuya cikin fasikanci da muguwar sha'awa ta jiki, an nuna su domin ishara, suna shan hukuncin madawwamiyar wuta.

8. Haka kuma masu mafarke-mafarken nan, sukan ƙazantar da jikinsu, su ƙi bin mulki, su kuma yi wa masu ɗaukaka baƙar magana.

9. Amma lokacin da babban mala'ika, Mika'ilu yake fama da Iblis, suna mūsu a kan gawar Musa, shi Mika'ilu bai yi garajen ɗora masa laifi da baƙar magana ba, sai dai ya ce, “Ubangiji yă tsawata maka.”

10. Amma mutanen nan sukan kushe duk abin da ba su fahinta ba, saboda abubuwan da suka sani bisa ga jiki suna kamar dabbobi marasa hankali, su ne kuwa sanadin halakarsu.

11. Kaitonsu! Don sun bi halin Kayinu, sun ɗunguma cikin bauɗewar Bal'amu don kwaɗayi, sun kuma hallaka ta irin tawayen Kora.

12. Waɗannan mutane kamar aibobi ne a taronku na soyayya, suna ta shagulgulan ciye-ciye a cikinku, ba kunya ba tsoro, suna kula da kansu kawai. Su kamar holoƙon hadiri ne, wanda iska take korawa. Su kamar itatuwa ne, marasa 'ya'ya da kaka, matattu murus, tumɓukakku.

13. Su kamar raƙuman ruwan teku ne masu hauka, suna taƙama da kumfar kunyarsu. Su kamar taurari ne masu kai da kawowa, waɗanda aka tanada wa matsanancin duhu har abada.

14. Anuhu ma wanda yake na bakwai daga Adamu, shi ma ya yi annabci a kan waɗannan mutane cewa, “Ga shi, Ubangiji ya zo da dubban tsarkakansa,

15. don ya zartar da hukunci kan kowa, yă kuma tabbatar wa marasa bin Allah dukan aikinsu na rashin bin Allah, da suka aikata ta hanyar rashin bin Allah, da kuma baƙaƙen maganganu da masu zunubi marasa bin Allah suka yi game da shi.”

16. Waɗannan su ne masu gunaguni, masu ƙunƙuni, masu biye wa muguwar sha'awa, marubata, masu yi wa mutane bambaɗanci don samun wata fa'ida.

17. Ya ku ƙaunatattuna, lalle ku tuna da maganar da manzannin Ubangijinmu Yesu Almasihu suka faɗa a dā,

18. da suka ce da ku, “A zamanin ƙarshe za a yi waɗansu mutane masu ba'a, masu biye wa muguwar sha'awarsu ta rashin bin Allah.”

19. Waɗannan su ne masu raba tsakani, masu son zuciya, marasa Ruhu.

20. Amma ya ku ƙaunatattuna, ku riƙa inganta kanku ga bangaskiyarku mafi tsarki, kuna addu'a da ikon Ruhu Mai Tsarki.

21. Ku tsaya a kan ƙaunar da Allah yake yi mana, kuna sauraron jinƙan Ubangijinmu Yesu Almasihu mai kaiwa ga rai madawwami.

Karanta cikakken babi Yahu 1