Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yahu 1:14-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Anuhu ma wanda yake na bakwai daga Adamu, shi ma ya yi annabci a kan waɗannan mutane cewa, “Ga shi, Ubangiji ya zo da dubban tsarkakansa,

15. don ya zartar da hukunci kan kowa, yă kuma tabbatar wa marasa bin Allah dukan aikinsu na rashin bin Allah, da suka aikata ta hanyar rashin bin Allah, da kuma baƙaƙen maganganu da masu zunubi marasa bin Allah suka yi game da shi.”

16. Waɗannan su ne masu gunaguni, masu ƙunƙuni, masu biye wa muguwar sha'awa, marubata, masu yi wa mutane bambaɗanci don samun wata fa'ida.

17. Ya ku ƙaunatattuna, lalle ku tuna da maganar da manzannin Ubangijinmu Yesu Almasihu suka faɗa a dā,

18. da suka ce da ku, “A zamanin ƙarshe za a yi waɗansu mutane masu ba'a, masu biye wa muguwar sha'awarsu ta rashin bin Allah.”

19. Waɗannan su ne masu raba tsakani, masu son zuciya, marasa Ruhu.

20. Amma ya ku ƙaunatattuna, ku riƙa inganta kanku ga bangaskiyarku mafi tsarki, kuna addu'a da ikon Ruhu Mai Tsarki.

21. Ku tsaya a kan ƙaunar da Allah yake yi mana, kuna sauraron jinƙan Ubangijinmu Yesu Almasihu mai kaiwa ga rai madawwami.

22. Ku ji tausayin waɗanda suke shakka,

23. kuna ceton waɗansu kuna fizgo su daga wuta. Waɗansu kuma ku ji tausayinsu, amma tare da tsoro kuna ƙyamar ko da tufafin da halinsu na mutuntaka ya ƙazantar.

24. Ga wanda yake da iko yă tsare ku daga faɗuwa, yă kuma miƙa ku marasa aibi a gaban ɗaukakarsa da matuƙar farin ciki,

25. ga Allah makaɗaici Mai Cetonmu ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu, ɗaukaka, da fifiko, da mulki, da iko su tabbata gare shi, tun fil'azal, da yanzu, da kuma har abada abadin. Amin, amin.

Karanta cikakken babi Yahu 1