Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yahu 1:11-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Kaitonsu! Don sun bi halin Kayinu, sun ɗunguma cikin bauɗewar Bal'amu don kwaɗayi, sun kuma hallaka ta irin tawayen Kora.

12. Waɗannan mutane kamar aibobi ne a taronku na soyayya, suna ta shagulgulan ciye-ciye a cikinku, ba kunya ba tsoro, suna kula da kansu kawai. Su kamar holoƙon hadiri ne, wanda iska take korawa. Su kamar itatuwa ne, marasa 'ya'ya da kaka, matattu murus, tumɓukakku.

13. Su kamar raƙuman ruwan teku ne masu hauka, suna taƙama da kumfar kunyarsu. Su kamar taurari ne masu kai da kawowa, waɗanda aka tanada wa matsanancin duhu har abada.

14. Anuhu ma wanda yake na bakwai daga Adamu, shi ma ya yi annabci a kan waɗannan mutane cewa, “Ga shi, Ubangiji ya zo da dubban tsarkakansa,

15. don ya zartar da hukunci kan kowa, yă kuma tabbatar wa marasa bin Allah dukan aikinsu na rashin bin Allah, da suka aikata ta hanyar rashin bin Allah, da kuma baƙaƙen maganganu da masu zunubi marasa bin Allah suka yi game da shi.”

16. Waɗannan su ne masu gunaguni, masu ƙunƙuni, masu biye wa muguwar sha'awa, marubata, masu yi wa mutane bambaɗanci don samun wata fa'ida.

17. Ya ku ƙaunatattuna, lalle ku tuna da maganar da manzannin Ubangijinmu Yesu Almasihu suka faɗa a dā,

18. da suka ce da ku, “A zamanin ƙarshe za a yi waɗansu mutane masu ba'a, masu biye wa muguwar sha'awarsu ta rashin bin Allah.”

Karanta cikakken babi Yahu 1