Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yahu 1:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Daga Yahuza bawan Yesu Almasihu, ɗan'uwan Yakubu zuwa ga kirayayyu, ƙaunatattun Allah Uba, keɓaɓɓu ga Yesu Almasihu.

2. Jinƙai, da salama, da ƙauna su yawaita a gare ku.

3. Ya ku ƙaunatattuna, da yake dā ma ina ɗokin rubuto muku zancen ceton nan namu, mu duka, sai na ga wajibi ne in rubuto muku in gargaɗe ku, ku dage ƙwarai a kan bangaskiyar nan da aka danƙa wa tsarkaka sau ɗaya tak, ba ƙari.

4. Gama waɗansu mutane sun saɗaɗo a cikinku, waɗanda tun zamanin dā aka ƙaddara ga hukuncin nan, marasa bin Allah ne, masu mai da alherin Allah dalilin aikata fajirci, suna kuma ƙin makaɗaicin Ubangijinmu Yesu Almasihu.

5. Sai dai ina so in tuna muku, ko da yake kun riga kun san kome sosai, cewa Ubangiji ya ceci jama'a daga ƙasar Masar, duk da haka daga baya ya hallaka waɗanda ba su ba da gaskiya ba.

6. Har ma mala'ikun da ba su kiyaye girmansu ba, amma suka bar ainihin mazauninsu, ya tsare su cikin sarƙa madawwamiya a baƙin duhu, har ya zuwa shari'ar babbar ranar nan.

7. Haka kuma Saduma da Gwamrata, da birane kewayensu, waɗanda su ma suka dulmuya cikin fasikanci da muguwar sha'awa ta jiki, an nuna su domin ishara, suna shan hukuncin madawwamiyar wuta.

8. Haka kuma masu mafarke-mafarken nan, sukan ƙazantar da jikinsu, su ƙi bin mulki, su kuma yi wa masu ɗaukaka baƙar magana.

9. Amma lokacin da babban mala'ika, Mika'ilu yake fama da Iblis, suna mūsu a kan gawar Musa, shi Mika'ilu bai yi garajen ɗora masa laifi da baƙar magana ba, sai dai ya ce, “Ubangiji yă tsawata maka.”

Karanta cikakken babi Yahu 1