Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 9:8-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Maƙwabta da waɗanda suka saba ganinsa dā yana bara, suka ce, “Ashe, ba wannan ne yakan zauna yana bara ba?”

9. Waɗansu suka ce, “Shi ne mana.” Waɗansu kuwa suka ce, “A'a, kai dai, sun yi kama.” Shi kuwa ya ce, “Sosai ni ne!”

10. Sai suka ce masa, “To, ƙaƙa aka yi idanunka suka buɗe?”

11. Ya amsa ya ce, “Mutumin nan da ake kira Yesu ne ya cuɗa ƙasa ya shafa mini a idanu, ya ce mini, ‘Je ka Siluwam ka wanke ido.’ Na kuwa je na wanke, sai na sami gani.”

12. Suka ce masa, “Ina yake?” Ya ce, “Ban sani ba.”

13. Sai suka kai wa Farisiyawa mutumin da yake makaho a dā.

14. To, ran Asabar ne Yesu ya cuɗa ƙasar ya buɗe masa ido.

15. Farisiyawa ma suka tambaye shi ta yadda aka yi ya sami gani. Ya ce musu, “Cuɗaɗɗiyar ƙasa ya shafa a idona, na wanke, ina gani.”

16. Saboda haka, waɗansu Farisiyawa suka ce, “Mutumin nan ba daga Allah yake ba, don ba ya kiyaye Asabar.” Waɗansu kuwa suka ce, “Yaya mutum mai zunubi zai iya yin mu'ujizai haka?” Sai rabuwa ta shiga tsakaninsu.

17. Sai suka sāke ce wa makahon, “To, kai fa, me ka gani game da shi, da yake kai ya buɗe wa ido?” Ya ce, “Ai, annabi ne.”

18. Yahudawa kam, ba su gaskata shi makaho ne a dā ba, ya kuma sami gani, har suka kira iyayen wanda ya sami ganin,

19. suka tambaye su suka ce, “Wannan ɗanku ne da kuke cewa an haife shi makaho? To, ta yaya yake iya gani yanzu?”

20. Sai iyayen nasa suka amsa suka ce, “Mun dai san wannan ɗanmu ne, makaho ne aka haife shi.

21. Amma ta yadda aka yi yake gani yanzu ba mu sani ba, ba mu ma san wanda ya buɗe idon ba. Ku tambaye shi, ai, ba yaro ba ne, zai faɗa da bakinsa.”

22. Iyayensa sun faɗi haka ne don tsoron Yahudawa, don dā ma Yahudawa sun ƙulla, cewa kowa ya amsa, cewa shi ne Almasihu, za a fisshe shi daga jama'a.

23. Shi ya sa iyayensa suka ce, “Ai, ba yaro ba ne, ku tambaye shi.”

Karanta cikakken babi Yah 9