Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 9:30-41 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. Sai mutumin ya amsa musu ya ce, “Yau ga abin mamaki! Ashe, ba ku san ta inda ya fito ba, ga shi kuwa, ya buɗe mini ido!

31. Mun sani Allah ba ya sauraron masu zunubi, amma duk wanda yake mai bautar Allah, yake kuma aikata nufinsa, Allah yakan saurare shi.

32. Tun da aka fara duniya ba a taɓa jin wani ya buɗe idon wanda aka haifa makaho ba.

33. Da mutumin nan ba daga Allah ya fito ba, da ba abin da zai iya yi.”

34. Suka amsa masa suka ce, “Kai da aka haifa a baƙin zunubi ne za ka koya mana?” Sai suka kore shi.

35. Yesu ya ji labari sun kore shi. Da ya same shi, ya ce, “Ka gaskata da Ɗan Mutum ko?”

36. Ya amsa ya ce, “Wane ne shi, ya Shugaba, da zan gaskata da shi?”

37. Yesu ya ce masa, “Ai, ka gan shi, shi ne ma mai magana da kai.”

38. Sai ya ce, “Ya Ubangiji, na ba da gaskiya,” ya kuma yi masa sujada.

39. Yesu ya ce, “Na shigo duniyan nan ne don rarrabewa, domin waɗanda ba sa gani su gani, waɗanda suke gani kuma su makance.”

40. Da Farisiyawan nan da suke tare da shi suka ji haka, suka ce masa, “Wato mu ma makafi ne?”

41. Yesu ya ce musu, “Ai, da makafi ne ku, da ba ku da zunubi. Amma da yake kun ce kuna gani, to, zunubinku ya tabbata.

Karanta cikakken babi Yah 9