Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 9:21-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Amma ta yadda aka yi yake gani yanzu ba mu sani ba, ba mu ma san wanda ya buɗe idon ba. Ku tambaye shi, ai, ba yaro ba ne, zai faɗa da bakinsa.”

22. Iyayensa sun faɗi haka ne don tsoron Yahudawa, don dā ma Yahudawa sun ƙulla, cewa kowa ya amsa, cewa shi ne Almasihu, za a fisshe shi daga jama'a.

23. Shi ya sa iyayensa suka ce, “Ai, ba yaro ba ne, ku tambaye shi.”

24. Sai suka sāke kiran mutumin nan da yake makaho a dā, suka ce masa, “Ka tsoraci Allah dai! Mu kam, mun san mutumin nan mai zunubi ne.”

25. Sai ya amsa ya ce, “Ko mai zunubi ne, ni ban sani ba. Abu ɗaya kam, na sani, dā ni makaho ne, yanzu kuwa ina gani.”

26. Sai suka ce masa, “Shin, me ya yi maka? Ta yaya ya buɗe maka ido?”

27. Ya amsa musu ya ce, “Na riga na faɗa muku, ba ku ji ba. Don me kuke so ku sāke ji? Ko ku ma kuna so ku zama almajiransa ne?”

28. Sai suka fāɗa shi da zagi, suna cewa, “Kai ne dai almajirin wannan ɗin, mu kam, almajiran Musa ne.

29. Mun dai sani Allah ya yi magana da Musa, amma wannan ba mu san ta inda ya fito ba.”

30. Sai mutumin ya amsa musu ya ce, “Yau ga abin mamaki! Ashe, ba ku san ta inda ya fito ba, ga shi kuwa, ya buɗe mini ido!

31. Mun sani Allah ba ya sauraron masu zunubi, amma duk wanda yake mai bautar Allah, yake kuma aikata nufinsa, Allah yakan saurare shi.

32. Tun da aka fara duniya ba a taɓa jin wani ya buɗe idon wanda aka haifa makaho ba.

33. Da mutumin nan ba daga Allah ya fito ba, da ba abin da zai iya yi.”

Karanta cikakken babi Yah 9