Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 9:16-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Saboda haka, waɗansu Farisiyawa suka ce, “Mutumin nan ba daga Allah yake ba, don ba ya kiyaye Asabar.” Waɗansu kuwa suka ce, “Yaya mutum mai zunubi zai iya yin mu'ujizai haka?” Sai rabuwa ta shiga tsakaninsu.

17. Sai suka sāke ce wa makahon, “To, kai fa, me ka gani game da shi, da yake kai ya buɗe wa ido?” Ya ce, “Ai, annabi ne.”

18. Yahudawa kam, ba su gaskata shi makaho ne a dā ba, ya kuma sami gani, har suka kira iyayen wanda ya sami ganin,

19. suka tambaye su suka ce, “Wannan ɗanku ne da kuke cewa an haife shi makaho? To, ta yaya yake iya gani yanzu?”

20. Sai iyayen nasa suka amsa suka ce, “Mun dai san wannan ɗanmu ne, makaho ne aka haife shi.

21. Amma ta yadda aka yi yake gani yanzu ba mu sani ba, ba mu ma san wanda ya buɗe idon ba. Ku tambaye shi, ai, ba yaro ba ne, zai faɗa da bakinsa.”

22. Iyayensa sun faɗi haka ne don tsoron Yahudawa, don dā ma Yahudawa sun ƙulla, cewa kowa ya amsa, cewa shi ne Almasihu, za a fisshe shi daga jama'a.

23. Shi ya sa iyayensa suka ce, “Ai, ba yaro ba ne, ku tambaye shi.”

24. Sai suka sāke kiran mutumin nan da yake makaho a dā, suka ce masa, “Ka tsoraci Allah dai! Mu kam, mun san mutumin nan mai zunubi ne.”

25. Sai ya amsa ya ce, “Ko mai zunubi ne, ni ban sani ba. Abu ɗaya kam, na sani, dā ni makaho ne, yanzu kuwa ina gani.”

26. Sai suka ce masa, “Shin, me ya yi maka? Ta yaya ya buɗe maka ido?”

27. Ya amsa musu ya ce, “Na riga na faɗa muku, ba ku ji ba. Don me kuke so ku sāke ji? Ko ku ma kuna so ku zama almajiransa ne?”

Karanta cikakken babi Yah 9