Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 9:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yesu na wucewa sai ya ga wani mutum da aka haifa makaho.

2. Sai almajiransa suka tambaye shi suka ce, “Ya Shugaba, wa ya yi zunubi da aka haifi mutumin nan makaho, shi, ko iyayensa?”

3. Yesu ya amsa ya ce, “Ba domin mutumin nan ko iyayensa sun yi zunubi ba, sai domin a nuna aikin Allah ne a kansa.

4. Lalle ne mu yi aikin wanda ya aiko ni tun da sauran rana. Ai, dare zai yi sa'ad da ba mai iya aiki.

5. Muddin ina duniya ni ne hasken duniya.”

6. Da ya faɗi haka sai ya tofa yau a ƙasa, ya cuɗa ƙasa, ya shafa a idanun makahon,

7. ya ce masa, “Je ka, ka wanke ido a ruwan Siluwam,” wato aikakke. Shi ke nan sai ya je ya wanke ido, ya komo yana gani.

8. Maƙwabta da waɗanda suka saba ganinsa dā yana bara, suka ce, “Ashe, ba wannan ne yakan zauna yana bara ba?”

9. Waɗansu suka ce, “Shi ne mana.” Waɗansu kuwa suka ce, “A'a, kai dai, sun yi kama.” Shi kuwa ya ce, “Sosai ni ne!”

10. Sai suka ce masa, “To, ƙaƙa aka yi idanunka suka buɗe?”

11. Ya amsa ya ce, “Mutumin nan da ake kira Yesu ne ya cuɗa ƙasa ya shafa mini a idanu, ya ce mini, ‘Je ka Siluwam ka wanke ido.’ Na kuwa je na wanke, sai na sami gani.”

Karanta cikakken babi Yah 9