Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 8:26-41 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. Akwai abubuwa da yawa da zan faɗa game da ku, in kuma hukunta. Amma shi wannan da ya aiko ni mai gaskiya ne. Abin da na jiyo daga gare shi kuwa, shi nake shaida wa duniya.”

27. Ba su gane maganar Uba yake yi musu ba.

28. Sai Yesu ya ce, “Sa'ad da kuka ɗaga Ɗan Mutum, a sa'an nan ne za ku gane ni ne shi, ba na yin kome kuma ni kaɗai, sai dai Uba ya koya mini, haka nake faɗa.

29. Wanda kuwa ya aiko ni yana tare da ni, bai bar ni ni kaɗai ba, domin koyaushe ina aikata abin da yake so.”

30. Sa'ad da Yesu yake faɗar haka, mutane da yawa suka gaskata da shi.

31. Sai Yesu ya ce wa Yahudawan nan da suka gaskata shi, “In dai kun zauna kan maganata, hakika ku almajiraina ne.

32. Za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za ta 'yanta ku.”

33. Suka amsa masa suka ce, “Ai, mu zuriyar Ibrahim ne, ba mu taɓa bauta wa kowa ba. Yaya kuma za ka ce za a 'yanta mu?”

34. Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, duk mai aikata zunubi bawan zunubi ne.

35. Ai, bawa ba ya ɗorewa a gida har abada, ɗa kuwa yana ɗorewa.

36. In kuwa Ɗan ya 'yanta ku, za ku 'yantu, 'yantuwar gaske.

37. Na san dai ku zuriyar Ibrahim ne, amma kuwa kuna neman kashe ni, don maganata ba ta shigarku.

38. Ina faɗar abin da na gani a wurin Ubana, ku kuma kuna yin abin da kuka ji daga wurin naku uba.”

39. Suka amsa masa suka ce, “Ai, Ibrahim ne ubanmu.” Yesu ya ce musu, “Da ku 'ya'yan Ibrahim ne, da sai ku yi aikin da Ibrahim ya yi.

40. Ga shi yanzu, kuna neman kashe ni, ni mutumin da na gaya muku gaskiyar da na ji wurin Allah. Ba haka Ibrahim ya yi ba.

41. Ku kuna aikin da ubanku yake yi ne.” Suka ce masa, “Ba a haife mu daga fasikanci ba, ubanmu ɗaya ne, wato Allah.”

Karanta cikakken babi Yah 8