Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 8:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yesu kuwa ya hau Dutsen Zaitun.

2. Da sassafe kuma ya sāke shiga Haikali. Duk mutane suka zo wurinsa, ya kuwa zauna yana koya musu.

3. Sai malaman Attaura da Farisiyawa suka kawo wata mace da aka kama da zina. Da suka tsai da ita a tsaka,

4. suka ce masa, “Malam, matan nan an kama ta ne, suna cikin yin zina.

5. To, a Attaura Musa ya umarce mu mu kashe irin waɗannan da jifa, kai kuwa me ka ce?”

6. Sun faɗi haka ne don su gwada shi, ko sa sami hanyar kai ƙararsa. Amma Yesu ya sunkuya, ya yi ta rubutu a ƙasa da yatsa.

7. Da suka dinga tambayarsa sai ya ɗaga, ya ce musu, “To, marar zunubi a cikinku ya fara jifanta da dutse.”

8. Sai ya sāke sunkuyawa, ya yi ta rubutu a ƙasa.

9. Su kuwa da suka ji haka suka fita da ɗaya ɗaya, tun daga babbansu har ya zuwa ƙaraminsu, aka bar Yesu shi kaɗai, da matar tsaye a tsakiya.

10. Sai Yesu ya ɗaga, ya ce mata, “Uwargida, ina suke? Ba wanda ya hukunta ki?”

11. Ta ce, “Babu, ya Ubangiji.” Sai Yesu ya ce, “Ni ma ban hukunta ki ba. Yi tafiyarki. Daga yau kada ki ƙara yin zunubi.”]

12. Sai Yesu ya ƙara musu da cewa, “Ni ne Hasken duniya. Wanda yake bi na ba zai yi tafiya a duhu ba, amma zai sami hasken rai,”

Karanta cikakken babi Yah 8