Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 6:62-71 Littafi Mai Tsarki (HAU)

62. Yaya ke nan in kuka ga Ɗan Mutum yana hawa inda yake dā?

63. Ai, Ruhu shi ne mai rayarwa, jiki kam ba ya amfana kome. Kalmomin da na faɗa muku ruhu ne, da kuma rai.

64. Amma fa akwai waɗansunku da ba su ba da gaskiya ba.” Domin tun farko Yesu ya san waɗanda ba su ba da gaskiya ba, da kuma wanda zai bāshe shi.

65. Sai ya ƙara da cewa, “Shi ya sa na gaya muku, ba mai iya zuwa gare ni, sai ko Uba ya yardar masa.”

66. Kan wannan da yawa daga cikin almajiransa suka koma da baya, ba su ƙara tafiya tare da shi ba.

67. Sai Yesu ya ce wa goma sha biyun, “Ku ma kuna so ku tafi ne?”

68. Bitrus ya amsa masa ya ce, “Ya Ubangiji, gun wa za mu je? Kai kake da maganar rai madawwami.

69. Mu kuwa mun gaskata, mun kuma tabbata kai ne Mai Tsarkin nan na Allah.”

70. Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba ni na zaɓe ku, ku goma sha biyu ba? To, ɗayanku Iblis ne.”

71. Wato, yana nufin Yahuza, ɗan Saminu Iskariyoti, don shi ne zai bāshe shi, ko da yake ɗaya daga cikin goma sha biyun nan ne.

Karanta cikakken babi Yah 6