Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 6:55-64 Littafi Mai Tsarki (HAU)

55. Domin naman jikina abinci ne na hakika, jinina kuma abin sha ne na hakika.

56. Duk wanda suke cin naman jikina, yake shan jinina, a cikina yake zaune, ni kuma a cikinsa.

57. Kamar yadda rayayyen Uba ya aiko ni, nake kuma rayuwa saboda Uban, haka ma wanda yake ni ne abincinsa zai rayu saboda ni.

58. Wannan shi ne Gurasan da ya sauko daga Sama, ba irin wadda kakannin kakanninku suka ci ba, duk da haka suka mutu. Duk mai cin Gurasan nan zai rayu har abada.”

59. Wannan kuwa a majami'a ya faɗa, sa'ad da yake koyarwa a Kafarnahum.

60. Da jin haka, da yawa daga cikin almajiransa suka ce, “Wannan magana mai wuya ce, wa zai iya jinta?”

61. Yesu kuwa, da yake ya sani a ransa almajiransa suna gunagunin wannan, sai ya ce musu, “Wato, wannan ne ya zamar muku abin tuntuɓe?

62. Yaya ke nan in kuka ga Ɗan Mutum yana hawa inda yake dā?

63. Ai, Ruhu shi ne mai rayarwa, jiki kam ba ya amfana kome. Kalmomin da na faɗa muku ruhu ne, da kuma rai.

64. Amma fa akwai waɗansunku da ba su ba da gaskiya ba.” Domin tun farko Yesu ya san waɗanda ba su ba da gaskiya ba, da kuma wanda zai bāshe shi.

Karanta cikakken babi Yah 6