Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 6:45-54 Littafi Mai Tsarki (HAU)

45. A rubuce yake cikin littattafan annabawa cewa, ‘Dukkansu Allah ne zai koya musu.’ To, duk wanda ya ji, ya kuma koya wurin Uba, zai zo gare ni.

46. Ba wai don wani ya taɓa ganin Uban, sai shi wanda yake daga wurin Allah, shi ne ya ga Uban.

47. Lalle hakika ina gaya muku, wanda ya ba da gaskiya, yana da rai madawwami.

48. Ni ne Gurasa mai ba da rai.

49. Kakannin kakanninku sun ci manna a jeji, amma kuwa sun mutu.

50. Ga Gurasa mai saukowa daga Sama, domin kowa yă ci, kada ya mutu.

51. Ni ne Gurasan rai da ya sauko daga Sama. Kowa ya ci Gurasan nan, zai rayu har abada. Har ma gurasar da zan bayar naman jikina ne, domin duniya ta rayu.”

52. Sai Yahudawa suka ta da husuma a junansu, suna cewa, “Yaya mutumin nan zai iya ba mu naman jikinsa mu ci?”

53. Sai Yesu ya ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, in ba ku ci naman jikin Ɗan Mutum ba, kuka kuma sha jininsa, ba rai a gare ku.

54. Duk wanda suke cin naman jikina, yake kuma shan jinina, yana da rai madawwami, ni kuwa zan tashe shi a ranar ƙarshe.

Karanta cikakken babi Yah 6