Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 6:34-46 Littafi Mai Tsarki (HAU)

34. Sai suka ce masa, “Ya Ubangiji, ka riƙa ba mu irin wannan gurasa kullum!”

35. Yesu ya ce musu, “Ni ne gurasa mai ba da rai. Wanda ya zo gare ni ba zai ji yunwa ba har abada, wanda kuma ya gaskata da ni ba zai ƙara jin ƙishirwa ba har abada.

36. Na dai gaya muku, kun gan ni, duk da haka ba ku ba da gaskiya ba.

37. Duk wanda Uba ya ba ni zai zo gare ni, wanda kuwa ya zo gare ni ba zan kore shi ba ko kaɗan.

38. Domin na sauko daga Sama, ba domin in bi nufin kaina ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni.

39. Nufin wanda ya aiko ni kuwa, shi ne kada in yar da kowa daga cikin dukkan waɗanda ya ba ni, sai dai in tashe su a ranar ƙarshe.

40. Gama nufin Ubana, shi ne duk wanda yake duban Ɗan, yake kuma gaskatawa da shi, yă sami rai madawwani, ni kuma zan tashe shi a ranar ƙarshe.”

41. Sai fa Yahudawa suka yi masa gunaguni, domin ya ce, “Ni ne Gurasan da ya sauko daga Sama.”

42. Suka ce, “Ashe, wannan ba Yesu ba ne, ɗan Yusufu, wanda uwa tasa da ubansa duk mun san su? To, yaya yanzu zai ce, ‘Na sauko ne daga sama’?”

43. Yesu ya amsa musu ya ce, “Kada ku yi gunaguni a junanku.

44. Ba mai iya zuwa wurina, sai dai in Uba wanda ya aiko ni ne ya jawo shi, ni kuwa zan tashe shi a ranar ƙarshe.

45. A rubuce yake cikin littattafan annabawa cewa, ‘Dukkansu Allah ne zai koya musu.’ To, duk wanda ya ji, ya kuma koya wurin Uba, zai zo gare ni.

46. Ba wai don wani ya taɓa ganin Uban, sai shi wanda yake daga wurin Allah, shi ne ya ga Uban.

Karanta cikakken babi Yah 6