Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 6:17-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Suka shiga jirgi suka tasar wa haye tekun zuwa Kafarnahun. A sa'an nan duhu ya yi, Yesu kuwa bai zo wurinsu ba tukuna.

18. Sai tekun ta fara hauka saboda wata riƙaƙƙiyar iska da take busowa.

19. Bayan sun yi tuƙi wajen mil uku ko huɗu, sai suka hango Yesu yana tafiya a kan ruwan, ya kusato jirgin. Sai suka firgita.

20. Amma ya ce musu, “Ni ne, kada ku ji tsoro.”

21. Sa'an nan suka yarda suka karɓe shi a cikin jirgin. Nan da nan sai ga jirgin a gāɓar da za su.

22. Kashegari sauran taron da suka tsaya a hayin tekun suka lura ba wani jirgi a wurin, sai wani ɗan ƙarami, suka kuma lura Yesu bai shiga cikinsa tare da almajiransa ba, sai almajiran ne kaɗai suka tafi.

23. Akwai kuwa waɗansu ƙananan jirage daga Tibariya da suka iso kusa da wurin nan da taron suka ci gurasa bayan Ubangiji ya yi godiya.

24. Sa'ad da kuwa taron suka ga ba Yesu, ba almajiransa a nan, su ma suka shiga ƙananan jiragen, suka tafi Kafarnahum neman Yesu.

25. Da suka same shi a hayin tekun, suka ce masa, “Ya Shugaba, yaushe ka zo nan?”

26. Yesu ya amsa musu ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, kuna nemana ne ba don kun ga mu'ujizai ba, sai don kun ci gurasar nan kun ƙoshi.

27. Kada ku yi wahala a kan neman abinci mai lalacewa, sai dai a kan abinci mai dawwama har ya zuwa rai madawwami, wanda Ɗan Mutum zai ba ku. Domin shi ne wanda Uba, wato Allah, ya tabbatar wa da ikon yin haka.”

28. Sai suka ce masa, “Me za mu yi mu aikata ayyukan da Allah yake so?”

Karanta cikakken babi Yah 6