Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 5:6-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Da Yesu ya gan shi kwance, ya kuma sani ya daɗe da wannan hali, sai ya ce masa, “Kana so a warkar da kai?”

7. Marar lafiyar ya amsa masa ya ce, “Ya Shugaba, ai, ba ni da wanda zai angaza ni cikin ruwan lokacin da aka motsa shi. Lokacin da na doshi ruwan kuma sai wani ya riga ni shiga.”

8. Sai Yesu ya ce masa, “Tashi, ka ɗauki shimfiɗarka, ka yi tafiya!”

9. Nan take mutumin ya warke, ya ɗauki shimfiɗarsa ya yi tafiya tasa.Ran nan kuwa Asabar ce.

10. Saboda haka Yahudawa suka ce da wanda aka warkar ɗin, “Ai, Asabar ce, bai kuwa halatta ka ɗauki shimfiɗarka ba.”

11. Sai ya amsa musu ya ce, “Ai, wanda ya warkar da ni, shi ne ya ce in ɗauki shimfiɗata, in tafi.”

12. Suka tambaye shi, “Wane mutum ne ya ce maka ka ɗauki shimfiɗarka ka tafi?”

13. Wanda aka warkar ɗin kuwa bai san ko wane ne ba, domin Yesu ya riga ya tashi saboda taron da yake wurin.

14. Bayan haka Yesu ya same shi a Haikali, ya ce masa, “Ka ga fa, ka warke! To, ka daina yin zunubi, don kada wani abu da ya fi wannan muni ya same ka.”

15. Sai mutumin ya tafi ya gaya wa Yahudawa, Yesu ne ya warkar da shi.

16. Saboda haka, Yahudawa suka fara tsananta wa Yesu, don yana yin irin waɗannan abubuwa ran Asabar.

17. Yesu kuwa ya amsa musu ya ce, “Ubana yana aiki har yanzu, ni ma ina yi.”

Karanta cikakken babi Yah 5