Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 5:42-47 Littafi Mai Tsarki (HAU)

42. Amma fa na san ku, ba ku da ƙaunar Allah a zuci.

43. Ni na zo ne da sunan Ubana, ga shi, ba ku karɓe ni ba. In da wani zai zo da sunan kansa, shi za ku karɓa.

44. Ta yaya za ku ba da gaskiya, ku da kuke karɓar girma a junanku, girman da yake daga Allah Makaɗaici kuwa, ba kwa nemansa?

45. Kada ku zaci zan yi ƙararku wurin Uba. Akwai mai yin ƙararku, shi ne Musa, wanda kuke dogara da shi.

46. Da dai kun gaskata Musa, da kun gaskata ni, domin labarina ya rubuta.

47. In kuwa ba ku gaskata abin da ya rubuta ba, ta yaya za ku gaskata maganata?”

Karanta cikakken babi Yah 5