Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 5:21-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Yadda Uba yake ta da matattu ya kuma raya su, haka Ɗan ma yake rayar da wanda ya nufa.

22. Uba ba ya hukunta kowa, sai dai yā danƙa dukkan hukunci ga Ɗan,

23. domin kowa yă girmama Ɗan, kamar yadda ake girmama Uban. Wanda ba ya girmama Ɗan, ba ya girmama Uban da ya aiko shi ke nan.

24. Lalle hakika, ina gaya muku, duk mai jin maganata, yake kuma gaskata wanda ya aiko ni, yana da rai madawwami. Ba za a yi masa hukunci ba, domin ya riga ya tsere wa mutuwa, ya kai ga rai.

25. “Lalle hakika, ina gaya muku, lokaci na zuwa, har ma ya yi, da matattu za su ji muryar Ɗan Allah, masu ji kuwa su rayu.

26. Yadda Uba kansa yake tushen rai, haka ya sa Ɗan ya zama tushen rai.

27. Ya kuma ba shi ikon zartar da hukunci, saboda shi Ɗan Mutum ne.

28. Kada ku yi mamakin wannan, domin lokaci na zuwa da duk waɗanda suke kaburbura za su ji murya tasa,

29. su kuma fito, waɗanda suka aikata nagarta su tashi, tashin rai, waɗanda suka yi rashin gaskiya kuwa su tashi, tashin hukunci.

30. “Ba na iya yin kome ni kaɗai. Yadda nake ji, haka nake yin hukunci. Hukuncina kuwa na adalci ne, domin ba nufin kaina nake bi ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni.

31. In na shaida kaina, shaidata ba tabbatacciya ba ce.

32. Akwai wani mashaidina dabam, na kuwa san shaidar da yake yi mini tabbatacciya ce.

33. Kun aika wajen Yahaya, shi kuma ya shaidi gaskiya.

34. Duk da haka shaidar da na dogara da ita ba ta mutum ba ce. Na dai faɗi haka ne domin ku sami ceto.

Karanta cikakken babi Yah 5