Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 5:1-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan haka aka yi wani idi na Yahudawa, Yesu kuwa ya tafi Urushalima.

2. A Urushalima, kusa da Ƙofar Tumaki, akwai wani ruwa da ake ce da shi Betasda da Yahudanci, an kuwa kewaye shi da shirayi biyar.

3. A shirayin nan kuwa marasa lafiya da yawa sun saba kwanciya, makafi, da guragu, da shanyayyu. [Suna jira a motsa ruwan.

4. Don lokaci lokaci wani mala'ika yakan sauko cikin ruwan ya motsa shi. Duk kuwa wanda ya fara shiga bayan an motsa ruwan, sai ya warke daga duk irin cutar da yake da ita.]

5. A nan kuwa akwai wani mutum da ya shekara talatin da takwas da rashin lafiya.

6. Da Yesu ya gan shi kwance, ya kuma sani ya daɗe da wannan hali, sai ya ce masa, “Kana so a warkar da kai?”

7. Marar lafiyar ya amsa masa ya ce, “Ya Shugaba, ai, ba ni da wanda zai angaza ni cikin ruwan lokacin da aka motsa shi. Lokacin da na doshi ruwan kuma sai wani ya riga ni shiga.”

8. Sai Yesu ya ce masa, “Tashi, ka ɗauki shimfiɗarka, ka yi tafiya!”

9. Nan take mutumin ya warke, ya ɗauki shimfiɗarsa ya yi tafiya tasa.Ran nan kuwa Asabar ce.

10. Saboda haka Yahudawa suka ce da wanda aka warkar ɗin, “Ai, Asabar ce, bai kuwa halatta ka ɗauki shimfiɗarka ba.”

11. Sai ya amsa musu ya ce, “Ai, wanda ya warkar da ni, shi ne ya ce in ɗauki shimfiɗata, in tafi.”

12. Suka tambaye shi, “Wane mutum ne ya ce maka ka ɗauki shimfiɗarka ka tafi?”

13. Wanda aka warkar ɗin kuwa bai san ko wane ne ba, domin Yesu ya riga ya tashi saboda taron da yake wurin.

14. Bayan haka Yesu ya same shi a Haikali, ya ce masa, “Ka ga fa, ka warke! To, ka daina yin zunubi, don kada wani abu da ya fi wannan muni ya same ka.”

15. Sai mutumin ya tafi ya gaya wa Yahudawa, Yesu ne ya warkar da shi.

Karanta cikakken babi Yah 5