Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 4:23-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Amma lokaci na zuwa, har ma ya yi, da masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a ruhu, da gaskiya kuma. Lalle kuwa irin waɗannan masu sujada ne Uba yake nema.

24. Allah Ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa lalle su yi masa sujada a ruhu, da gaskiya kuma.”

25. Sai matar ta ce masa, “Na san Masihi yana zuwa, wanda ake kira Almasihu. Sa'ad da ya zo kuwa, zai sanar da mu kome.”

26. Yesu ya ce mata, “Ni ne, ni mai maganan nan da yake.”

27. Nan take almajiransa suka dawo. Suka yi mamakin ganin yana magana da mace. Amma kuwa ba wanda ya ce, “Me kike bukata?” ko, “Don me kake magana da ita?”

28. Sai matar ta bar tulunta, ta koma gari, ta ce wa mutane,

29. “Ku zo, ku ga mutumin da ya gaya mini duk abin da na taɓa yi! Shin, ko wannan shi ne Almasihu?”

30. Sai suka fito daga garin suka nufo shi.

31. Ana cikin haka sai almajiran suka roƙe shi suka ce, “Ya shugaba, ci abinci.”

32. Amma ya ce musu, “Ina da abincin da ba ku sani ba.”

33. Almajiran suka ce wa juna, “Shin, wani ya kawo masa abinci ne?”

34. Sai Yesu ya ce musu, “Abincina shi ne in aikata nufin wanda ya aiko ni, in kuma cika aikinsa.

Karanta cikakken babi Yah 4