Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 3:9-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Sai Nikodimu ya amsa masa ya ce, “Ƙaƙa wannan zai yiwu?”

10. Yesu ya amsa masa ya ce, “Ashe, kai ma da kake malamin Isra'ila, ba ka fahimci waɗannan al'amura ba?

11. Lalle hakika, ina gaya maka, abin da muka sani shi muke faɗa, muna kuma shaidar da abin da muka gani, amma kun ƙi yarda da shaidarmu.

12. In na yi muku zancen al'amuran duniya ba ku gaskata ba, yaya za ku gaskata in na yi muku zancen al'amuran sama?

13. Ba wanda ya taɓa hawa cikin Sama sai shi wanda ya sauko daga Sama, wato, Ɗan Mutum da yake Sama.

14. Kamar yadda Musa ya ɗaga macijin nan a jeji, haka kuma dole ne a ɗaga Ɗan Mutum,

15. domin duk wanda ya gaskata da shi, ya sami rai madawwami.

16. “Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya hallaka, sai dai ya sami rai madawwami.

17. Gama Allah bai aiko Ɗansa duniya domin yă yanke mata hukunci ba, sai dai domin duniya ta sami ceto ta wurinsa.

18. Duk wanda ya gaskata da shi, ba za a yi masa hukunci ba. Wanda kuwa bai ba da gaskiya ba, an riga an yi masa hukunci, domin bai gaskata da sunan makaɗaicin Ɗan Allah ba.

Karanta cikakken babi Yah 3